Da misalin karfe 9:32 na safiyar yau, a gogon Kasar, Saraki ya isa Kotun yayin da kuma 'Yan Majalisar Dattawa 50 da wasu mambobin Majalisar wakilan Kasar suka yi masa rakiya zuwa Kotun.
Daga cikin 'Yan Majalisar Dattawan da suka raka shi, akwai Theodore Orji, Sam Egwu, Ike Ekweremadu, Shaba Lafiaji, Aliyu Wamako, Hamma Misau da Sabi Aliyu Abdullah.
A farko dai Saraki ya ki bayyana a gaban kotun, al-amarin da ya sa ta bada sammacin kama shi harma ta bukaci Babban Speto Janar na Yan Sandan Najeriya da ya taso mata keyarsa matukar ya gagara bayyana a gabanta a yau talata. 289